Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwamishinan ƴan sandan jihar kano ya bijirewa umarnin mu – gwamna Abba

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana damuwarta kan matakin da kwamishinan ƴan sandan jihar ya dauka, wanda ake zarginsa da kin bin umarnin gwamna, musamman dangane da hana bukukuwan Sallah babba.

Wannan na ƙunshe ne yayin zantawa da manema labarai da ya gudanar a gidan gwamnatin jihar a ɗakin taro na Afrika House, wanda kwamishinan shari’a na jihar Barista Haruna Isa Dederi, ya yi tsokaci kan al’amuran da ke faruwa, inda ya ce, “An tilasta min in sake yi muku jawabi a madadin mai girma Gwamna.

“A ranar 23 ga Mayu, 2024, Majalisar Dokokin Jihar ta zartar da kudirin, wanda ba tare da bata lokaci ba Gwamnan ya sanya hannu kan dokar bayan kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki da jami’an tsaro.”

Kwamishinan Shari’a da yayi jawabi a madadin Gwamna Abba Yusuf ya bayyana cewa duk da matakan da aka dauka ana zargin wasu mutane da yunkurin tada zaune tsaye a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa, “Wasu mutane na yin kakkausar suka don ganin an hukunta mutanen Kano bisa rashin adalci saboda siyasa” in ji sanarwar, yayin da take magana kan soke dokar Masarautar ta 2019 da kuma ƙarar da ta biyo baya.

Gwamnatin ta kuma yi tsokaci kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya mai lamba 3 da ke Kano ta yanke a baya-bayan nan, inda ta ce an tauye muhimman hakkokin tsohon sarkin, ciki har da zargin dauri.

Gwamnatin Jihar Kano dai ta musanta hakan, inda ta ce, “Ba wanda ya tilasta masa shiga Gidan Nassarawa, mallakar gwamnatin Jihar Kano, Ya shiga can ya zauna bisa raɗin kansa tare da rakiyar jami’an tsaro, Don haka babu wanda ya saka shi a gidan.”

Gwamnati ta jaddada hakkin da tsarin mulki ya ba Gwamna a matsayin babban jami’in tsaro na jihar don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi.

“Lokacin da tsohon sarkin ya shigo tare da rakiyar wasu ɓata gari suna barazana ga zaman lafiya a jihar, domin tabbatar da zaman lafiya shiyasa gwamnan ya bayar da umarnin kama shi,” in ji sanarwar.

Haka kuma gwamnantin ta nuna damuwa game da matakin da Kwamishinan ƴan sandan ya dauka, musamman matakin daya dauka na hana bukukuwan sallah babba ba tare da tuntubar Gwamna ko Majalisar Tsaro ta Jihar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!