Labarai
Kwamishinan kasafin kuɗi na Kano ya yi murabus don takarar majalisar tarayya
Kwamishinan kasafin kuɗi na jihar Kano Alhaji Nura Muhammad Ɗankadai ya sauka daga muƙaminsa don takarar majalisar tarayya mai wakiltar Tudunwada da Doguwa.
Mai taimakawa Gwamnan kan kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Gwamna Ganduje ya bai wa masu riƙe da muƙaman siyasa da ke sha’awar takara umarnin ajiye aiki domin biyayya ga dokar zaɓe.
You must be logged in to post a comment Login