Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kwamishinan muhalli ya ja kunne hukumomin asibiti kan tsabtar muhallinsu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi hukumomin asibitin Sir Sunusi sakamakon halin rashin tsafta da suka nuna a wasu sassan asibitin.

Kwamishinan muhalli Nasiru Sule Garo ne yayi gargadin lokacin da ya kai ziyarar duban tsaftar muhalli asibitin a yau.

Wanda ya ce, abin takaici ne yadda ake zubar da sharar allurai da magunguna a cikin asibitin wanda hakan ke barazana ga lafiyar al’umma.

Da yake karin bayani kan yadda ya samu hukumar KNARDA da KNUPDA, Nasiru Sule Garo ya bukaci su da su dauki matakan kula da banɗakunan su da kuma kawar da shara a hukumomin.

Freedom Radio ta tawaito cewa, ma’aikatar muhalli ta bukaci unguwanni da za su yi aikin gayya a gobe da su sanar da ita don ba su kayan aiki da kuma kwashe dattin a kan lokaci.

Rahoton: Madeena Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!