Labarai
Kwamishinan sufiri na Kano ya sauka domin takarar majalisar tarayya
Kwamishinan sufiri na Kano Alhaji Mahmud Muhammad Santsi ya ajiye muƙaminsa domin takarar ɗan majalisar tarayya a ƙananan hukumomin Gabasawa da Gezawa.
Mai taimakawa Gwamnan kan kafafen sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Gwamna Ganduje ya bai wa masu riƙe da muƙaman siyasa da ke sha’awar takara umarnin ajiye aiki domin biyayya ga dokar zaɓe.
Kawo yanzu Kwamishinoni bakwai ne suka ajiye muƙamansu a yau, tare da wasu hadiman Gwamnati da zimmar tsayawa takara.
You must be logged in to post a comment Login