Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya kai tallafi ga ‘yan gudun hijira

Published

on

Kwmishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Habu Ahmad Sani, ya ziyarci Makarantar yara ‘yan gudun hijira da ke mariri tare da kai musu tallafin kayan abinci da na sana’o’in dogaro da kai.

Kwamishinan na wannan ziyara ne a ci gaba da bikin murnar cikarsa shekara daya a matsayin kwaminan ‘yan sandan jihar Kano.

Habu Ahmad Sani, yayin ziyarar yayi alkawarin ci gaba da bin duk wasu hanyoyi da tsarin aikin dan sanda ya tanadar domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

A nasa jawabin Babban malami a Makarantar ‘yan gudun hijirar Malam Usman Rabe, ya godewa Kwamishinan bisa tallafawa marayun.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!