Labarai
Kwamitin Ma’aikatar Shari’a ya gano ƙarrakin da ke buƙatar kammala su da wuri

Kwamitin da ma’aikatar shari’a ta kafa domin gano manyan shari’un da suka jima ba a kawo karshen su ba, ya gano wasu manyan shari’o’i da ke buƙatar a kammala su cikin gaggawa.
Kwamishinan Shari’a, Barista Abdulkarim Kabiru Maude SAN, ne ya kafa kwamatin don kawo karshen shari’un da aka dade ana yinsu, tare da rage cunkosan jama’a a gidajen gyaran hali.
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran ma’aikatar Najib Lawan Danbazau, ya fitar ga manema labarai.
Sanatwar ta ce, kwamatin mai mambobi 7 karkashin jagorancin Barista Rabi’at Sa’ad Sule, ya fara aikin sa da ziyartar kotunan majistare na Gyadi-Gyadi inda ya ziyarci kotuna 7 daga cikin goma sha biyar da ke yankin.
A yayin ziyarar, kwamitin ya gano wasu shari’o’in da suka dade ba a kawo karshen su ba, tare da bukatar sakeyin nazari a kansu.
Sanarwar ta ƙara da cewa, yayin ziyarar shugabar kwamitin Barista Rabi’at Sa’ad Sule, ta yaba da jajircewar ma’aikatan kotu, tana mai cewa kwamitin na da nufin gano matsaloli da samar da mafita domin tabbatar da ingantaccen tsarin shari’a a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login