Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Kwamitin yaki da cutar COVID-19 zai fallasa sunayen wadanda sukayi biris da dokar killace kai a Najeriya

Published

on

Kwamitin dake yaki da cutar COVID 19 ya ce zai fallasa sunayen mutane casa’in da suka dawo daga kasashen waje kuma suka ki bin dokokin killace kai domin gujewa sake barkewar cutar a fadin kasar nan.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana hakan yayin zatanwa da manema labarai.

A cewar Boss Mustapha mutanan sun dawo ne daga kasahen Turkiya da Indiya da Birazil tsakanin ranakun 8 zuwa 15 ga wannan watan da muke ciki.

Ya kara da cewa wanda sukaki amincewa su killace kawunan nasu da kuma kin amincewa anyi musu gwaji sun sauka ne a filayen jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos sai kuma filin jirgin sama na Nnamdi azikwiwema dake birin tarayya Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!