Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masarautar Katsina ta nada sabon hakimin karamar hukumar Kankara

Published

on

Masarautar Katsina, ta sanar da sunan Alhaji Adamu Bello, a matsayin sabon hakimin Kankara, bayan sauke tsohon hakimin Alhaji Yusuf Lawal, da aka zarge shi da taimakawa masu garkuwa da mutane.

Hakan na kunshe a cikin takardar nadin sabon hakimin mai dauke da sa hannun sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, mai dauke da kwanan watan 24 ga Mayu.

A cewar sakataren masarautar Sarkin Yakin Katsina, Alh. Bello Mamman-Ifo, ya tabbatar da cewar bayan kafa kwamitin bincike a samu tsohon hakimin da laifi na taimakawa ‘yan ta’adda tare da lalata yunkurin jami’an tsaro wajen samar da zaman lafiya da kare dukiyar jama’a a yankin nasa.

A baya dai masarautar ta Katsina ta sauke dagacin mai sarautar Sarkin Fauwan Katsina hakimin Kankara, bisa zargin sa da taimakwa ‘yan bindigar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!