Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwankwasiya ce tafi yawan magoya baya a PDP – Kwankwaso

Published

on

Jagoran Jami’iyyar PDP Sanata Rabi’u Musa Kwankwasiyya ya ce, tarin magoya baya da tsagin na su ke da shi ya sanya jami’iyyarsu ke ci gaba da samun ci gaba a faɗin Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya gudanar a a gidan radion Nasara a ranar Laraba.

Kwankwaso wanda tsohon gwamna Kano ne ya ce “jami’iyyar PDP muna zaton ta yi duba da yadda Kwankwasiyya ke da tarin magoya baya ba iya jihar Kano ko arewaci ko Najeriyar ba ma gaba ɗaya.

“Zaben shugabannin jami’iyyar PDP na Arewa maso yammaci da aka samu rikici yayin gudanar da shi wanda jami’iyyar daga baya ta aminta da baiwa ɓangaren na Kwankwasiyya kujerun duba da yadda tsagin ke da tarin magoya baya” a cewar Kwankwaso

Kwankwaso ya kuma ce “Yadda PDP ta yi tunanin amincewa da baiwa tsaginmu shugabanci sakamakon idan jami’iyyar tana so ta yi nasarar lashe zaɓen 2023 to sai ta samu nasarar jihohin Rivers da Lagos da kuma Kano, wanda idan ba’a tafi da mu a jami’iyyar ba to samun nasara ba zai yiwu ba”

A watannin da suka gaba dai PDP ta shirya gudanar da zaɓen shugabbanin jami’iyyar na shiyyar arewa maso gabas da a ƙarshe aka samu rikice-rikece yayin taro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!