Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Siyasa ba da gaba ba: Ganduje ya taya Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwar sa

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon gwamna Sanata Rabi’u Musa kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Gwanduja ya taya shi murna ne ta cikin wani saƙo da aka wallafa a jaridar Daily Trust da safiyar ranar Alhamis, da ya aikewa Kwanksawo da ke bayyana sakon taya shi murnar zagayowar haihuwar sa.

Saƙon na ƙunshe da cewa “A madadi na da iyalai na da gwamnati na da sauran al’ummar Kano muna taya ka murnar cika shekara 65”.

Ni da kaina naje EFCC ba kamani suka yi ba-Kwankwaso

Ta cikin saƙon Ganduje ya ci gaba da cewa “Tabbas Kwankwaso ka taka rawar gani wajen ciyar da jihar Kano gaba lokacin da kake riƙe da kujerar gwamna ni kuma ina matsayin mataimaki a don haka ba za mu taɓa mantawa da irin wannan gudunmawa ba”.

Ta cikin saƙon Ganduje ya yi fatan samun ingantacciyar lafiya da kwanciyar hankali ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Wannan dai na cikin sanarwar da mai taimakawa gwamna Ganduje kan harkokin kafofin sada zumunta Abubakar Aminu Ibrahim ya fitar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!