Connect with us

Labarai

Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP nan take.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, inda ya ce matakin da ya dauka ba karamin abu ba ne, duba da rawar da ya taka a jam’iyyar tsawon lokaci.

 

Ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa la’akari da halin da siyasar Najeriya ke ciki a yanzu, wanda ke bukatar sake tsari da kuma neman wata sabuwar hanya da za ta ba shi damar kawo sauyi a kasar.

 

Tsohon gwamnan ya kuma gode wa shugabannin jam’iyyar, ciki har da shugabanta na kasa, da kwamitocin ta, bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake cikin jam’iyyar.

Haka kuma, ya yabawa mambobin kungiyar Kwankwasiyya da magoya bayansa bisa jajircewarsu da goyon bayan da suka bayar.

Kwankwaso ya kara da cewa zai ci gaba da hada kai da masu ruwa da tsaki domin ganin an samar da makoma mai kyau ga Najeriya.

Rahotanni na nuni da cewa ana sa ran zai koma wata jam’iyya daban a cikin mako mai zuwa, a wani mataki na sauyin siyasa gabanin babban zaben 2027.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!