Connect with us

Labarai

Duk mai son aikin dan sanda sai ya cika ka’idojin rundunar – IGP

Published

on

Sufeton ‘yan sanda na kasa Muhammad Adamu ya ce ka’idojin da rundunar ta shimfida wajen shiga aiki suna nan daram, kuma shakka babu sai kowa ya bi su kafin shiga tsarin aikin na dan sanda.

Muhammad Adamu ya ce ya zama wajibi duk mai shirin shiga aikin dan sanda ya cika ka’idojin da aka zayyana a sashe na 71 zuwa 75 na kundin dokokin hukumar ‘yan sanda.

Ya kara da cewa, duk matashin da yayi nasara a yayin cike fam din shiga aikin dan sanda na Internet, to za’a gayyace shi don tantancewa da aka fara tun daga jiya 24 ga watan da muke ciki na Agusta, zuwa 6 ga watan Satumba a cibiyoyi daban-daban dake fadin kasar nan.

Sufeton ‘yan sanda Muhammad Adamu ya kuma hori jami’an dake tantancewar da su maida hankali, wajen baiwa duk wanda ya cika ka’ida damar da kundin dokokin hukumar ‘yan sanda ta tsara su bashi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!