Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kyautatawa mabukata zai taimaka wajen ragi radadi- Sarkin Alkalman Kano

Published

on

Sarkin Alkalman Kano Alhaji Ilyasu Labaran Daneji, ya shawarci mawadatan jihar Kano da su kara kaimi wajen tallafawa masu karamin karfi duba da cewa gwamnati ta hana shigowa Kano da fita domin rage musu radadi sakamakon annobar cutar Covid 19.

Alhaji Ilyasu Labaran Daneji ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai kan annobar cutar Corona domin fadakar da mutane kan yadda zasu kare kansu daga cutar da kuma tabbatar da cewa coronavirus ba ta shigo Kano ba.

Ya kuma ce, nauyi ya yiwa gwamnati yawa don haka kamata yayi mutane masu hannu da shuni da su rika ba da nasu gudunmawar.

Alhaji Ilyasu Labaran ya kuma bukaci mutane da su rika daukar kwararan matakai da kuma yin addu’oi don neman dauki daga wajen Al..h

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa, Sarkin Alkalma na Kano ya kuma shawarci jama’a da su rika tsaftace jikin su da kuma muhallan su kamar yadda masana kiwon lafiya su ke ba da shawara domin kare kansu daga cutar ta corona.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!