Labarai
Labarin Zakunan da suka taba ballewa a fadar shugaba Buhari.
A satin da muka yi bankwana da shi ne zaki ya balle daga kejinsa a gidan ajiye namun daji na jahar Kano, kafafan yada labarai da dama ne suka bayar da Labaran ballewar zakin daga gidan namun dajin na jahar Kano.
Rahotanni sun yi nuni da cewa wannan zaki ya koma ma’ajiyarsa da kansa duk da gayyato masu allurar kashe jiki ta manyan dabbobi irin su zaki da kwararru suka yi daga Abuja, da sauran gurare da aka yi gayyar.
Zakin na gidan adana namun dajin ya tayar da hankalin al’umma daban daban har su kansu al’ummar yankin basu samu kwanciyar hankali ba, sakamakon sanarwar cewa su kula da abunda kaje ya kawo kafin a kame zakin da garkame shi.
Manyan namun daji irin su zaki da zakanya na bukatar kula yadda ya kamata ,shin gidan namun daji na jahar Kano , wacce matsala da ya kamata a shawo kanta tun fil azal an yi nasara.
A zamanin mulkin Janar Abdussalami Abubakar rikakkun zakuna sun taba ballewa daga kejin da suke inda suka rika ruri a harabar fadar ta shugaban kasa ,har ta kai tsohon shugaban kasa janar Abdulsalami Abubakar hankalin sa ya kai ga zakunan da bayar da umarnin harbe su.
Malam Yahaya Zariya na daya daga cikin maaikatan fadar shugaban kasar Najeriya a lokacin da zakuna suka ballle a fadar.
A binciken tarihi da Freedom radio tayi ya nuna cewa Malam Yahaya na aiki a fadar shugaban kasa tun lokacin birnin tarayya na Legas, a fadar Dodan Barrack.
Lokacin da shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ya dawo da mazaunar Gwamnatin tarayya a Abuja malam Yahaya mutumin Zariya ya cigaba da aiki a lambun fadar Shugaban Najeriya.
Malam Yahaya yace a lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha an bashi kyautar jariran zakuna daga kasar Sierra leone zamanin mulkin Ahmad Tijjani Kabbah.
Sannan marigayi Shugaba Abacha ya siyo wasu jariran zakuna da Malam Yahaya ya cigaba da kula da su har suka rika.
A bibiyar Tarihin da gidan rediyan Freedom yayi tace lokacin da zakunan na fadar Shugaban Najeriyar suka rika kuma Malam Yahaya na kiwon su sai da masana ilimin dabbobin daji suka umarce shi da ya rage kusantar wadannan namun daji sakamakon rika da suka yi.
Mai kula da zakunan yace sakamakon sabawa da yayi da Zakunan na fadar shugaban kasa, bai daina kusantar suba domin shi yake ciyar da su abinci a wannan lokaci ta hanyar yanka musu raguna.
Malam Yahaya mai aiki a fadar ta shugaban kasa ya kara da cewa wata rana an samu kuskure a fadar ta shugaban Najeriya zamanin mulkin janar Abdulsalami Abubakar ,sai Zakunan suka balle aka kasa shawo kansu a fadar ta shugaban kasa.
Hakan ya jawo hankalin tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar inda ya bayar da umarnin rundunar sojan dake tsaran fadar ta shugaban kasa da su harbe Zakunan na fadar ta shugaban kasar.
Jin haka hankalin Malam Yahaya mutumin Zariya ya tashi saboda kaunar da yake yiwa wadannan zakuna.
Malam Yahaya ya yi ta maza, ya sai da rai, inda ya shiga kejin Zakunan na fadar shugaban kasa ya yi wa Zakunan kiranye sai suka biyo shi suka shiga ,shi kuma yayi sauri ya rufe kofar ya fuce ta wata.