Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Ladubban karatun Al-qur’ani da ya kamata ku sani – Dr. Nazafi

Published

on

Alqur’ani mai girma, maganar Allah ne, sannan kuma littafin sa ne mai girma, shi ba kamar sauran gamagarin maganganu bane, domin saukakke ne daga mai hikima abin godiya.

Don haka ne Allah madaukakin sarki ya shar’anta ma na wasu ladubba da ya wajaba mu lura da su wajen karatun Alqur’ani, domin girmama sha’anin sa, da daukaka matsayin sa.

Ya shar’antawa wanda zai karanta shi ya kasance mai tsarki, kuma ya kasance mai kankan da kai, tare da lura da tadabburin sa, da dai sauransu.

Yan uwa masu daraja, Hakika babu wata babbar ni’ima da Allah ya yiwa wannan al’ummah bayan ni’imar aiko da Annabi Muhammad (SAW) kamar ba mu Alqur’ani mai girma. Mu rike Alqur’ani domin riko da shi alkhairi ne duniya da lahira.

Domin ma’abocin karanta alqur’ani a kowanne lokaci z aka same shi cikin yalwar farin ciki, wofantar da shi kuma al’amari da ka iya jefa mutum a cikin rudanin rayuwa.

Allah ya saukar da Alqur’ani ta hanyar daya daga cikin Mala’iku, wato Mala’ika Jibrilu zuwa ga Annabi Muhammad (SAW).

Sanadiyyar haka, sai Mala’ika Jibril ya zama mafi alkhairi, kuma mafi falala da matsayi a cikin sauran Mala’iku, saboda falalar saukar da Alqur’anin ta wajen sa shi kadai.

Kuma Allah ya saukar da Alqur’ani mai girma a cikin watan Ramadan, sai watan Ramadan ya zamanto wata mafi girman alkhairi da falala a kan sauran watannin shekara baki daya.

Shiyasa Allah ya shar’anta mana yin azumi a wannan watan saboda falalar saukar da alqur’ani a cikin sa.

 

Malam Muhammad Nazifi Inuwa a yayin da yake gabatar da shirin azkar a tashar Freedom Radio Kano ya bayyana irin ladubban da mutum ya kamata yayi kafin ya fara karanta Alqur’ani:-

  1. Ya kasance mutum ya yi Aswaki kafin ya fara karanta Alqur’ani.
  2. Mutum ya kasance ya na da tsarki kafin karanta Alqur’ani.
  3. Ya kasance an daura alwala kafin fara karanta Alqur’ani.
  4. Saka tufafi masu kyau da saka turare mai kamshi kafin fara karanta Alqur’ani.
  5. Ya na da kyau mutum ya kalli alkibla yayin da zai karanta Alqur’ani.
  6. Yin karatu a fili ko kuma a boye kada ka damu mutane.
  7. Daga murya.
  8. Daukar Alqur’ni ko kuma yi da ka.
  9. Yin karatu da dadin murya, domin kyautata murya (Abu Musal Ash ari ya na karatu annabi ya ji ya ce, karatun al-qur’anin ka na da dadi, kamar murya Annabi Daudu, jiya ina jin ka muryar ka akwai dadi, sai Abu Musal Ash ari ya ce da na san kana nan da na sake daga murya).
  10. Banda yin riya.
  11. Banda yin sa kamar waka.
  12. Akwai yadda a ke yin na kari.
  13. Kada ka damu mutane da daddare ko na kusa da kai.
  14. Ana so ka fara daga kan gaba.
  15. Ka dinga gane ma’anar qur’ani.
  16. A dinga tsayawa a kan inda za ka tashi.
  17. Ka dinga tsayawa a kan Wakafi da Aya.
  18. Ina ya kamata mutum ya tsaya ya kuma tashi.
  19. Ya na da kyau idan ka fara karatun alqur’ani ka kammla.

Ba’a son ka dinga karatu da baragada

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!