Labarai
Lagos: Ƴan sanda sun kama mutane 5 bisa zarginsu da yin garkuwa da yaro

Rundunar ’yan sandan Jihar Lagos ta kama mutane biyar bisa zargin yin garkuwa da wani matashi dan karɓar kuɗin fansa.
A cikin sanarwar da mai magana yawun rundunar yan sandan jihar SP Abimbola Adebisi, ya fitar ya ce lamarin ya shafi wani ɗalibi mai suna Victor Aligwo, inda aka gano cewa shi da wasu abokansa huɗu ne suka shirya satar da kansa domin yaudarar mahaifiyarsa.
SP Adebisi ta ce, an yi bidiyon neman agaji na ƙarya domin tsoratar da mahaifiyar sa lamarin da ya sa ta biya naira miliyan 1.7 a matsayin kudin fansa.
You must be logged in to post a comment Login