Connect with us

Kiwon Lafiya

Lagos:kudan zuma sun kashe wani jami’in hukumar yaki da fasakwauri

Published

on

Kudan zuma sun kashe wani babban jami’in hukumar yaki da fasakwauri ta kasa, CUSTOM, mai suna Abba Abubakar.

 

Rahotanni sun ce Abba Abubakar wanda jami’in hukumar ta CUSTOM ne da ke aiki a ofishin hukumar da ke Seme daf da Badagry a jihar Lagos, kudan zuma sun kai mishi farmaki ne a shekaran jiya Talata.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar yaki da fasakwauri ta kasa mai kula da ofishin ta da ke Seme, Sai’du Abdullahi.

 

Sanarwar ta ce lamarin ya faru a shekaran jiya lokacin da jami’in ke baki aikin sa a yankin Ashipa a Badagry da ke jihar Lagos, inda anan ne kudan zuman suka mamaye shi.

 

Sanarwar ta kuma bayyana marigayin Abba Abubakar wanda dan asalin jihar Yobe ne a matsayin jajirtaccen ma’aikaci da ya sadaukar da ransa wajen aiki tukuru, ya mutu ne ya bar mata daya da ‘ya’ya da dama kuma tuni aka yi jana’izar sa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!