Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Lasisin tuƙa adaidaita sahu ya koma dubu ɗari a Kano – KAROTA

Published

on

Hukumar KAROTA ta ce, daga yanzu lasisin tuƙa adaidaita sahu a Kano ya koma Naira dubu ɗari maimakon dubu takwas da ake yi a baya.

Shugaban hukumar Baffa Babba Ɗanagundi ne ya sanar da hakan a yau Laraba yayin taron manema labarai.

Ya ce, duk wanda ba su yi rajistar neman iznin tuƙin a baya ba, to yanzu ya koma dubu ɗari.

Baffa Babba ya ƙara da cewa, jami’an su na ci gaba da lura domin ɗaukar mataki ga duk wanda aka samu bashi da lasisin.

A cewar sa, Gwamnati ta bayar da lokaci domin ayi rajistar amma, wasu masu kunnen ƙashi suka ƙi yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!