Labaran Kano
Lauyoyi sun koka kan rashin kotun daukaka kara a Kano
Wani kwararren lauya a nan Kano Barista Abbas Haladu Gawuna, ya bayyana cewa Kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yiwa gyara ya kirkiri kotuna tare da dokokin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tare da baiwa duk dan takarar da ba’a yi masa adalci ba a harkokin zabe ya garzyawa kotu domin neman hakkin sa.
Barista Abbas Haladu Gawuna, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin ‘’Duniyarmu a yau” na nan Freedom Radio wanda ya mayar da hankali kan hukunce-hukuncen da kotun sauraren korafin zabukan Kano ta yi a kwanakin baya.
Ya ce dokar ta bada dammar fara gabatar da korafin ne tun daga zaben fitar da gwani har bayan kammala zabe inda ake shigar da kara a Election Tribunal, wato kotun saurarran kararrakin zabe domin gabatar da shaidu da hujjoji.
Haka kuma ya kara da cewa ana shigar da korafin zaben ne cikin kwanaki 21 idan kuwa mutum yah aura hakan to ya sarayar da damar da kundin tsarin mulkin kasa ya bashi, inda daga nan ma ana iya daukaka kara idan hukunci bai yiwa mai korafi dadi ba.
Shi kuwa wani malami a shashen koyar da aikin lauya na jami’ar Bayero ta Kano Barista Dr. Muhammad Nuraddin, da ya kasance a cikin shirin ya bukaci da a samar da kotun daukaka kara a jihar Kano domin saukaka wa al’umma wajen samun damar cin gajiyar samun adalcin shari’a cikin sauki.
Haka kuma ya kara da cewa an kafa hukumar zabe ne tun a shekarar 1959 lokacin mulkin Turawa inda bayan kasar nan ta samu ‘yanci kai majalisar dokoki ta baiwa hukumar damar shirya zabuka ta duk hanyar da ta ga zaben zai inganta.