Connect with us

Labarai

Lauyoyin Kano sun shirya taron addu’o’i

Published

on

Kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano, ta bayyana cewa za ta gudanar da wani gagarumin taron adduoi daga ranar 25 zuwa 30 ga wannan wata da muke ciki na Oktoba.
Shugaban kwamitin shirya taron Barista Habibu Muhammad Faruk ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da Freedom Radio.
Barista Habibu Muhammad Faruk ya ce, ya yi taron dai za a gudanar da tattaki zuwa gidan gwamnatin Kano tare da yin salla da adduoin neman daukin uban giji bisa matsalolin da ake fama da su musamman na garkuwa da mutane da satar yara da sauransu.
Haka kuma ya kara da cewa, za su gayyato manyan lauyoyi da malamai da sauran masu ruwa da tsaki da za su bada gudunmawa wajen gudanar da taron.
Shugaban kwamitin shirya taron ya kara da cewa, makasudin shirya taron shi ne domin musulmi su taru don neman Allah ya jibanci labarin su kan magance matsalolin da Najeriya ta tsinci kanta ciki.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!