Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An dage cigaba da shari’ar zargin wacce ta tsallake rijiya da baya a Sauddiya

Published

on

Babbar kutun tarraya dake da zama a gyadi-gyadi dake nan Kano  karkashin jagoranci me shari’a lewis Allgoa ta dage sauraran shari’ar da ake zargin wasu mutune  shida  bisa sanyawa wata yarinya me suna Zainab Habibu Aliyu kwaya a cikin Jakarta a yayin da zata tafi kasa mai tsarki tare da iyayen ta.

An dai sanya ranakun 21 zuwa 22 ga  watan Nuwanban domin cigaba da shari’a, kan wannan zargin da ake yi wa wasu ma’aikatan filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Mutune shidan da’ake zargi sun hada da Idiris Umar  wanda aka fi  sani da Umar sanda da Sani  Suleman  da  Nuhu Adamu da kuma Rhoda Adetungi Udosen Itoro Henry, Sai kuma Sani Hamisu .

PDP ta yi korafi kan mai Shari’a Zainab Bulkachuwa

Kotu ta cigaba da sauraron shari’ar Malam Shekarau

An dage yanke hukunci a shari’ar takardun makarantar Shugaba Buhari

Haka kuma a jiya ne Lauyan hukumar hana sha da fataucin kwayoyi Barista Femi Oloruotumba ya gabatar da shedu biyu daya hada da wace tashirya tafiyar Hajiya Rabi Umar  wacce mahaifiya ce ga Zainab Aliyu tace tabaiwa me Auna kaya jakukkuna uku, yayin da suke shirye-shiryen zuwa kas amai tsarki

A cewar ta, ta baiwa mai suna Salisu Alasan Bako shi kuma yake tabbatar wa kotun cewar  Hajiya Rabi Umar tabashi jakukkuna uku da Fasfonan tafiye-tafiye uku kuma nan take ya  aike da su zuwa  daki matafiya, don tantancewa wanda bisa al’ada ake yi wa fasinjoji.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!