Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ranar Abinci ta duniya: Mai masana suka ce kan wannan?

Published

on

An dai fara gudanar da bikin ranar abinci ta duniya a shekarar 1945, da nufin wayar da kan al’umma a fadin duniya, irin matakan da suka kamata a dauka wajen yaki da yunwa da fari, ta hanyar samar da ingantaccen abincin ga al’umma.

Kudurin majalisar dinkin duniyar dai ya hada da taimaka mutane miliyan tamanin da shida da dubu dari bakwai da ke cikin kangin yunwa a cikin kasashen 83 na duniya a ko wace shekara.

Taimakon ya hada da rarraba mu su kayan abinci mai gina jiki da kuma aiki tare da al’ummomin yankunan na su don ganin komai ya tafi yadda ya kamata.

Freedom Rediyo ta tattauna da wasu mutane a nan Kano, domin jin ra’ayinsu a kan wannan rana.

Mutanen dai sun ce akwai matsalolin da kasar nan ke fuskanta wajen samar da abinci da inganata hanyoyin da za’a bunkasa ayyukan noma don ganin an wadata kasar nan da abinci

Wasu manoma da muka zanta da su sun bayyana irin kalubalen da suke fuskanta a lokacin noma da kuma bayan girbe amfanin gonar.

Farfesa Auwal Magashi Malami ne a tsangayar koyar da harkokin Noma a jami’ar Bayero da ke nan Kano, ya ce kamata ya yi manoma su fara neman shawarwarin masana kafin fara shiga duk wata harka ta noma.

Ya kuma kara da cewa yana da kyau manoma su rinka amfani da ingantattun iri na shuka, domin samun ingantattun kayayyakin abinci.

Taken bikin na bana dai shi ne ’’matakan da zamu dauka su ne samar da abinci mai gina jiki da kuma kawar da yunwa a duniya’’.

Majalisar dinkin duniya tare da hadin gwaiwar kungiyar nan ta kwararru a fannin harkokin gona ta duniya ne sun ware ranar 16 ga watan Oktoban ko wacce shekara, a matsayin ranar abinci ta duniya, domin tunawa da mutanen da suka tsinci kansu cikin matsanancin halin yunwa a fadin duniya.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!