Kiwon Lafiya
Likitocin Najeriya na shirin tsunduma yajin aiki a makon nan

Kungiyar Likitocin Njeriya NMA ta ce, zuwa ranar Alhamis mai zuwa idan har gwamnatin tarayya ba ta cika mata alkawuran da ta dauka ba, to za ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Shugaban kungiyar Farfesa Bala Audu, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Jaridar The Punch.
Ya kuma ce, kamar yadda gwamnatin ta yi wa kungiyar alkawari a zaman da suka gabatar a baya-bayan nan, kan za ta biya musu bukatun su kafin nan da ranar 23 ga watan da muke ciki na Yuli wanda zai kama ranar Alhamis din makon nan.
Shugaban kungiyar ta NMA ya kuma ce, suna yin hakan ne domin samar da gyara a fannin Lafiya da zai sa a samu yadda ake bukata wajen kula da lafiyar al’ummah.
You must be logged in to post a comment Login