Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Limami ya ɗaure ɗansa a gida tsawon shekaru 15 a Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kai samame gidan limamin Jumu’a na unguwar Fulani dake Sheka a ƙaramar hukumar Kumbotso.

Rahotonni sun bayyana cewa a yayin samamen ƴan sanda sun gano ɗan limamin mai suna Ibrahim Lawal da ake zargin mahaifinsa ya kulle shi har tsawon shekaru sha biyar.

Wata majiya mai tushe ta shaida mana cewa, ‘yan sanda basu samu limamin a gida ba, inda rahotonni suka ce limamin ya tafi ƙauye sai matarsa kaɗai ƴan sanda suka iske.

Har zuwa wannan lokaci dai rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ba ta yi ƙarin haske a kan lamarin ba.

Ko a watan Satumba na shekarar 2019 shirin Inda Ranka na gidan rediyon Freedom ya bankaɗo yadda wani mutum mai suna Muhammadu Ojudi dake garin Rinji a ƙaramar hukumar Madobi, ya kulle ƴaƴansa biyu da sarƙa har tsawon shekaru.

A ƙarshe Muhammadu Ojudi ya rasa ransa yayin da hukumomi ke dab da fara bincikarsa, daga bisani kuma jami’an lafiya a Kano suka tabbatar da cewa, ƴar sa guda ɗaya daga cikin waɗanda ya kulle ta samu taɓin hankali sanadiyyar wannan ɗauri.

Haka ma a ranar Larabar da ta gabata ƴan sanda sun ceto wani matashi a unguwar Farawa wanda mahaifinsa ya kulle shi tsawon shekaru bakwai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!