Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An ceto matashin da aka kulle a gida tsawon shekaru 7 a Kano

Published

on

Makwabta da haɗin kan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Right Network da kuma jami’an ‘yan sanda, sun samu nasarar kuɓutar da wani matashi da ake zargin mahaifinsa ya ɗaure shi a gida har tsawon shekaru 7.

Matashin mai suna Ahmad Aliyu mai shekaru 32 a duniya mazaunin Unguwar Farawa Babban layi a yankin ƙaramar hukumar ƙumbotso yana tsare ne har shekaru 7 ba tare da samun kulawar da ta dace ba, ta ci da sha da sutura kamar yadda wani daga cikin mutanen da suka yi ƙoƙarin ceto shin ya shaidawa Freedom Radio.

Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, mahaifin matashin ne ya killace shi a gida, tare da haɗin kan matarsa kasancewar mahaifiyarsa ta rasu, bisa yadda mahaifin nasa ya ce, ya fara shaye-shaye.

Haka kuma ya shaida wa Freedom Radio cewa, ko a yau da ‘yan ƙungiyar ta Human Right Network da DCO na ofishin ‘yan sanda na Farawa suka je gidan domin kuɓutar da matashin, matar mahaifin nasa ta ƙeƙasa ƙasa cewa baya gidan amma da suka kutsa kai ciki suka gano shi.

Wakilin mu Auwal Hassan Fagge da ya je ofishin’ yan sandan na Farawa, ya ruwaito cewa ya yi ido huɗu da matashin wanda saboda yunwa da ta ramar da shi har ta kai ga ba ya iya miƙewa tsaye.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!