Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

LMC ta zaftarewa Pillras maki uku bayan hatsaniya a wasanta da Katsina United

Published

on

Kamfanin shirya gasar firimiya na kasa LMC ya sake dauke Kano Pillarsa da ci gaba da buga wasa a filin Sani Abacha da ke kofar Mata na Kano.

Kamfanin na LMC ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi 17 ga Afrilun 2022 a wata wasika da ya ai kewa kungiyar ta Kano Pillars.

Haka zalika an kuma ci tarar kungiyar kudi Naira Miliyan tara bayan karya ka’idojojin hukumar da ke lura da gasar ta NPFL ta sanya.

Cikin hukuncin da akai wa Pillars an kuma mayar da ita filin wasa na MKO Abiola da ke birnin tarayya Abuja domin ci gaba da buga wasanninta na gida.

An kuma zarewa tawagar maki uku cikin maki 26 da take dashi.

Haka kuma an dakatar da filin wasa na Sani Abacha dake Kano daga karbar bakuncin wasan gasar NPFL har nan da wani lokaci.

A gefe guda kuma kungiyar Sai Masu gida zata gyarawa abokiyar hamayyarta Katsina United motarta da ta lalata Mata a wasan da suka fafata a ranar Asabar wasan da aka samu hatsaniya.

Za kuma a sanya ranar da kungiyar Pillars zata karasa wasanta da Katsina United a filin MKO Da ke birnin tarayya Abuja sakamakon rashin karasa wasan da ba aiba wanda aka tashi a minti na 89.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!