Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

FA Cup: Chelsea zata fafata da Liverpool a wasan karshe

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tayi nasar doke Crystal Palace da ci 2-0 a wasan kusa da karshe na gasar kofin kalu bale na kasar Ingila FA Cup.

Fafatawar da ta gudana a katafaren filin Wembley na kasar Ingila a ranar Lahadi 17 Afirilu, 2022, nasar da ta baiwa Chelsea damar kai wa wasan karshe a gasar.

Zakarun gasar cin kofin turai a kakar wasannin bara dai tayi rashin nasarar ficewa daga kofin turai a hannun Real Madrid a wasa gida da waje jumulla da ci 5-4.

Dan wasan Chelsea Mason Mount

A minti na 65 dan wasan tsakiyar Chelsea Ruben Loftus-Cheek ya fara zura kwallon farko, kana dan wasan kasar Ingila Mason Mount ya kara kwallo ta biyu a minti na 76 bayan samun tai mako daga hannun dan wasa Timo Werner.

Yanzu haka dai Chelsea zata kece raini da Liverpool wadda tayi nasarar doke Manchester City a wasan da suka fafata a ranar Asabar.

Wasan karshen zai gudana a katafren filin wasa na Wembley da ke birnin London a ranar 14 ga Mayun shekarar da muke ciki da misalin karfe 3 a gogon Najeriya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!