Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

LMC za ta wayar da kan kungiyoyi a kan lasisi

Published

on

Kamfanin shirya gasar League ta kasa, LMC ya shirya wayar da kan kungiyoyin gasar cin kofin kwararru ta kasa dangane da tattara bayanan neman lisisi.

Za dai su fara tattaunawar ne ta kafar sadarwa daga ranar 10 zuwa 18 ga wannan watan na Satumba da muke ciki.

Kamfanin na LMC ya bukaci daukacin kungiyoyin cikin gida da su kawo takardun neman lasisin wanda ya zama dole ga kungiyoyin dake bukatar shiga gasar cin kofin kwararru ta kasa a kakar wasanni ta 2020/2021.

Hakan ya biyo bayan sababbin dokoki da tsare-tsaren hukumar kwallon kafa ta kasa NFF tare da hadin kan hukumar kwallon kafa ta Afrika ta fara yi wa kowace kungiyar kwallon kafa rijistar lasisi.

Gudanar da rijistar lasisin da za’a fara ranar 18 ga wannan watan, zai taimakawa kungiyoyin gaya ta fannoni daban-daban a harkokin wasanni a fadin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!