Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

KAROTA: Mun gano jami’an bogi 45 – Baffa Babba

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta ce, ta gano ma’aikatan bogi sama da 45 da suke aiki a hukumar.

Shugaban hukumar Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radiyo.

Dan Agundi ya ce, tun bayan da wasu jami’an KAROTA suka yi ƙorafi kan zaftare musu albashi, hukumar ta tashi tsaye wajen binciken ma’aikatan kuma aka gano na bogi a ciki.

“Duk jami’in da yaga an zaftare albashin sa, to kuwa ba daga hukumar mu ba ne, sai ya bincika ko yaci bashin banki” in ji Baffa.

Baffa Babba ya kara da cewa, hukumar KAROTA za ta riƙa shirya bita ga  ma’aikatan ta akan yadda ya kamata su riƙi bi da masu ababen hawa ba tare da sun ci zarafin su ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!