Labarai
Ma’aikatan Hukumar samar da Ruwa ta Kano sun yi zanga-zanga

Kananan ma’aikatan Hukumar samar da Ruwa ta jihar Kano, sun gudanar da zanga-zanga a gaban zauren Majalisar Dokoki.
Ma’aikatan, sun yi wannan zanga-zanga ne a yau Litinin suna neman gwamnatin Kano ta shawo kan matsalolin da suka dade suna fuskanta.
Haka kuma, sun roki Majalisar Dokokin da ta sanya baki, tare da bukatar Gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf da ta dauki matakin gaggawa domin tabbatar da su, bayan da suka shafe shekaru 13 suna aikin wucin gadi.
A cewar su, tsawon lokacin da suka yi suna aiki ba tare da tabbatacciyar takardar daukar aiki ba, ya shafi rayuwarsu, tare da jefa su cikin halin rashin tabbas.
Majalisar Dokokin dai ta karɓi korafin, inda ta sha alwashin tattaunawa da hukumomin da lamarin ya shafa domin nemo mafita a kan lokaci, a cewar shugaban kwamitin hukumar bayar da ruwan sha, Musa Tahir Hungu.
You must be logged in to post a comment Login