Manyan Labarai
Ma’aikatan Jihar Kano ma su ritaya na bin Gwamnati fiye da Naira biliyan 17
Maaikatan gwamnatin jahar Kano da suka yi ritaya daga shekarar 2015 na bin gwamnatin jahar Kano fiye da Naira biliyan goma sha bakwai a matsayin kudaden sallama.
Danmajalisar jaha mai wakiltar karamar hukumar Dala a majalisar dokokin jahar Kano Lawal Cediyar Yangurasa ne ya bayyana haka lokacin shirin Barka da Hantsi na gidan Rediyan Freedom.
Danmajalisar wanda dan jami’yyar hamayya ne ta PDP yace a shekarar 2015 lokacin da Gwamnatin injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ta bar gwamnati, kudaden gratuti da ma’aikata masu ritaya ke bi Naira biliyan daya ne da miliyan dari daya kacal.
Lawal Cediyar “Yangurasa wanda Shi ne shugaban kwamitin harkokin ma’aikata da “yan fansho yace har yanzu akwai hukumomin da basa bayar da kason su na “yan fansho Wanda hakan yasa wasu daga cikin maaikatan jahar ta Kano suka shiga halin ni ‘ya su.
Lawal Cediyar ”Yan gurasa ya ce ko gidajen da tsohuwar gwamnatin jahar Kano ta gina na biranen Kwankwasiyya da Bandirawo da Amana a halin yanzu gwamnati ta karya farashin su .
Ya kara da cewa hakan ne ya saka ‘yan fasho suka shiga halin haula’i saboda yadda aka tsara biranen da siyar da su bai kai kudaden da aka tanada ba.