Labarai
Ma’aikatan Lafiya a Lagos sun tsunduma yajin aiki
Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan lafiya na jihar Lagos, sun sanar da tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga yau Laraba sakamakon gazawar gwamnatin jihar wajen fara biyansu a kan sabon tsarin mafi karancin albashi.
Kungiyoyin da suka amnice da shiga yajin aikin sun hada da Kungiyar jami’an jinya da Unguwan Zoma, da kungiyar kwararrun jami’an lafiya sai kungiyar likitoci da sauran jami’an lafiya da kuma gamnayyar kungiyoyin jami’an lafiya JOHESU.
Da ya ke yin karin haske kan tsunduma yajin aikin, sakataren Kungiyar jami’an jinya da Unguwan Zoma, Oloruntoba Odumosu, ya ce, daukar matakin ya biyo bayan karewar wa’adin da suka bai wa gwamnati amma ba ta yi komai a kai ba.
Haka kuma, ya ce, ko a ranar 9 ga wannan watan da muke ciki na Disamba, ba a cimma wata matsaya ba a ganawar da kungiyoyin jami’an lafiyar suka yi da jami’an gwamnatin jihar.
You must be logged in to post a comment Login