Kiwon Lafiya
Ma’aikatar lafiya ta tabbatar da ɓullar Kwalara a Kano
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta tabbatar da ɓullar cutar amai da gudawa a birnin Kano.
Babban jami’in kula da cututtuka masu yaɗuwa na ma’aikatar Sulaiman Iliyasu ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da Wakiliyar Freedom Radio Safara’u Tijjani Adam ta wayar tarho.
Ya ce an samu rahoton ɓullar cutar a ƙaramar hukumar Ɗanbatta wadda har aka samu asarar rayukan mutane biyu.
“A watan Afrilu mun samu rahoton ɓullar cutar amai da gudawa a Ɗanbatta wadda daga nan kuma sai cutar ta ɓulla a ƙaramar hukumar Gwarzo”.
Dr. Iliyasu ya ci gaba da cewa “Ya zuwa yanzu sama da mutane 25 zuwa 30 ne suka kamu da cutar a ƙwaryar birnin Kano kamar yadda sakamakon gwajin da muka yi ya tabbatar”.
A cewar jami’in a yanzu haka ƙananan hukumomin da suka samu ɓullar cutar sun haɗa da: karamar hukumar Dala da Ungoggo ƙaramar hukumar birni sai kuma Tarauni.
Dr. Sulaiman Isyaku ya buƙaci al’umma da su ƙara kula da tsaftar muhallansu da kuma kai rahoton duk wata cuta da ta ɓulla ga hukumomin lafiya don ɗaukan matakin gaggawa
You must be logged in to post a comment Login