Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu yi bincike kan bullar cutar mashako- ma’aikatar lafiya

Published

on

Bayan da aka samu rade-radin bular cutar mashako ta dheptaria a karamar hukumar Munjibir, hukumar Lafiya ta jihar Kano tayi Karin haske akan rade-radin.

Wannan na zuwa ne lokacin da dama daga cikin al’ummar jihar Kano basu da masaniya akan yadda cutar ta take, a gefe guda kuma masana ke bayyana illolin dake tattare da cutar.

Masana harkokin lafiyar na cewa ita wannan cuta nau’in cuta ce irin su mura da kenda da take sarke numfashi wadda idan ba’ayi hanzarin neman magani ba kan iya salwantar da ran dan Adam.

Wasu mutane da freedom radiyo ta zanta da su sun shaida mana cewa basu ma san ma yadda cutar take ba, ko kuma alamun ta.

Abdullahi Isamail Kwalwa mai sharhi ne kuma Jami’in kiwon lafiya a nan kano , yayi Karin haske kan yadda cutar ta mashako take.

Masanin ya kuma kara da cewa alamomin cutar a fili suke kuma cut ace dake barazana ga kowa.

Dakta Imam Wada Bello shi ne Daraktan hukumar dakile cutittika masu yaduwa a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, ya ce kafin ace an samu barkewa ko kuma annobar cuta, ya ce bisa ka’ida dole ne sai an gudanar da gwaje-gwaje da kuma tabbatar da adadin mutanen da suka kamu da cutar.

Ko da muka tuntubi hukumar lafiya ta jihar Kano ta bakin mai Magana da yawunta Abdullahi Ibrahim, cewa yayi suna kan bincike kan rade-radin bular cutar kuma zasu magantu anan gaba da zarar sun kammala binciken su.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!