Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ma’aikatar wasanni ta bada umarnin dawowa gasar firimiyar kwallon Kwando ta Najeriya

Published

on

Ma’aikatar matasa da wasanni ta Najeriya ta amincewa hukumar kwallon kwando ta kasa NBBF da ta dawo cigaba da shirya gasar league ta maza da aka dakatar tsawon shekaru.

Wannan umarnin na zuwa ne bayan da Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori karar da Hukumar Gudanar da kwallon kwando ta Kwese ta shigar a gabanta ta na kalubalantar ma’aikatar ta NBBF.

A cikin wata takarda dauke da sa hannun Babban Sakataren ma’aikatar Nebeolisa Anako, ma’aikatar ta baiwa NBBF damar fara kowace gasa a fadin kasar nan.

“Duba da wannan hukuncin da aka yanke, yanzu hukumar ta kara kaimi wajen neman masu daukar nauyin gasar maza bayan da Kwese ta zanye hannunta sakamakon matsalar kudade,” a cewar NBBF.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!