Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

CAF: Ya zama wajibi Afirka ta lashe kofin duniya – Motsepe

Published

on

Sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka Patrice Motsepe, ya ce, ya zama dole daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa na Afirka ya lashe gasar cin kofin duniya a wannan lokacin.

Motsepe mai shekara 59 ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Johannesburg dake kasar Afirka ta kudu.

“Sababbin tsare-tsaren da za mu kawo, a nan gaba kadan muna da yakinin cewa wata kungiya a nahiyar Afirka za ta lashe kofin duniya,” inji sabon shugaban.

An dai zabi Patrice Motsepe a matsayin shugaban hukumar ta CAF a makon da ya gabata bayan da aka hana tsohon shugaban Ahmad Ahmad neman tazarce bisa matsalolin shugabanci.

Motsepe ya kuma dauki alkawarin sauka daga mukamin nasa matukar ya gaza kawo ci gaba a hukumar bayan shekaru hudu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!