Connect with us

Labarai

Mace-macen aure su ne manyan kalubalen da muke fuskanta – Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce mace-mace aure da sauran matsalolin auren na daga cikin manyan kalubalan da suke fuskanta a cikin aikinsu.

Mukaddashiyar Kwamnandan hukumar mai kula da bangaren mata Malama UmmuKulsum Kassim ce ta bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio, wanda ya yi duba kan matsalolin zamantakewar aure wanda aka yi a jiya Juma’a.

Malama Ummukulsum ta kara da cewa rashin daukar ragamar kula da iyalai daga bangaren mazaje na daga cikin abubuwan da ke haddasa wannan matsala.

Ta kara da cewa wajibi ne mazaje su rinka taimakawa mata wajen tarbiyyantar ‘ya’yansu domin bunkasa rayuwarsu.

Malama UmmuKulsum Kassim ta shawarci iyaye su dage sosai wajen baiwa ‘ya’yansu ilimin addinin musulunci yadda ya dace domin kyautata rayuwarsu a nan duniya da kuma gobe kiyama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!