Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje zai dauki matakin ladaftarwa akan shugabannin tashar mota

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta baiwa shugabannin tashar mota ta Rijiyar Zaki wa’adin mako guda da su tabbatar da tsaftace ciki da wajenta, ko kuma ta dauki matakin ladaftarwa a kansu.

Kwamishinan muhalli na Jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya ba da umarnin yayin duban tsaftar muhalli na kasuwanni da asibitoci da ma’aikatun gwamnati, wanda ake gudanarwa a karshen ko wane wata.

Kwamishinan wanda babban sakatare a ma’aikatar Adamu Abdu Faragai ya wakilta, ya ce gwamnati ba za ta lamunci barin datti a wuraren hada-hadar jama’a ba, a don haka za ta dauki mataki kan masu karya dokar tsaftar muhalli.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!