Labarai
Mafi yawan haramtattun makaman da ake shigowa da su kasar nan na da alaka da jami’an tsaron kasashe makwabta – Kwamado Jamila
Wata babbar jami’ar sojin ruwan kasar nan Kwamado Jamila Abubakar ta yi zargin cewa akasarin haramtattun makaman da ake satar shigowa da su kasar nan na da alaka da jami’an tsaron kasashe makwabta.
Kwamado Jamila Abubakar, na yin wannan zargi ne lokacin da ta wakilci babban Kwamandan sojojin ruwan kasar Auwal Zubairu Gambo, ya yin zaman sauraron jin ra’ayoyin jama’a da kwamitin majalisa kan harkokin tsaron kasa da tattara bayanan sirri ya gudanar.
Ta ce gudunmanwar makaman da ake baiwa makotan kasar nan shi ke kwararowa Najeriya yana kuma zama barazana.
Sai dai Sha’aban Saharada da ke zaman shugaban kwamitin harkokin tattara bayanan sirri a majalisar wakilain ya ce, zargin jami’ar bai zo da mamaki ba la’akari da yadda tsaro yake a kasar nan.
Ya ce, sun karbi bayanan za su nazarci gaskiyar batutuwan da ta gabatar da zarge-zargenta a kai.
You must be logged in to post a comment Login