Connect with us

Labarai

Mafi yawan haramtattun makaman da ake shigowa da su kasar nan  na da alaka da jami’an tsaron kasashe makwabta – Kwamado Jamila

Published

on

Wata babbar jami’ar sojin ruwan kasar nan Kwamado Jamila Abubakar ta yi zargin cewa akasarin haramtattun makaman da ake satar shigowa da su kasar nan na da alaka da jami’an tsaron kasashe makwabta.

Kwamado Jamila Abubakar, na yin wannan zargi ne lokacin da ta wakilci babban Kwamandan sojojin ruwan kasar Auwal Zubairu Gambo, ya yin zaman sauraron jin ra’ayoyin jama’a da kwamitin majalisa kan harkokin tsaron kasa da tattara bayanan sirri ya gudanar.

Ta ce gudunmanwar makaman da ake baiwa makotan kasar nan shi ke kwararowa Najeriya yana kuma zama barazana.

Sai dai Sha’aban Saharada da ke zaman shugaban kwamitin harkokin tattara bayanan sirri a majalisar wakilain ya ce, zargin jami’ar bai zo da mamaki ba la’akari da yadda tsaro yake a kasar nan.

Ya ce, sun karbi bayanan za su nazarci gaskiyar batutuwan da ta gabatar da zarge-zargenta a kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!