Labaran Kano
Magidanci ya kashe dansa a Kano
Rundunar Yansanda ta Kano ta samu nasarar cafke wani magidanci bisa kashe dansa dan kimanin shekara uku .
Magidancin mai suna Musbahu mazaunin unguwar mahaukaci dake karamar hukamar Gaya ya zubawa dan nasa shinkafar bera a cikin abinci sanadiyyar haka ne yaron ya rasu.
A zantawar da wakilin mu Abba Isa Muhammad yayi da magidancin ya bayyana cewa ya aikata haka ne soboda yasamu yaran ne bata hanyar aure ba kuma ba shi da mahaifiya da zata rike masa yaron shi yasa ya kasha dan,amma kuma ya nemi da a sassauta masa bisa abun da ya aikata.
Kakakin rundunar yansanda ta Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa yace da zarar sun gama bincike zasu mika mai lefin zuwa Kotu domin ya fuskanci hukunci.