Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Wata kungiya ta shirya babban taron matasan jihar Kano

Published

on

Kungiyar dake rajin ganin an dama da matasa a bangaren siyasa da ke Jihar Kano mai suna Kano Youths Political Forum ta bukaci shugabanni a duk matakai da su ci gaba da bawa matasa mukamai domin su tallafa wajen samar da ci gaba mai dorewa.

Shugaban kungiyar Mukhtar Dauda Raula ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyara da kungiyar ta kawo tashar Freedom, gabanin babban taron matasan jihar Kano da kungiyar ta shirya.

Mukhtar Dauda Raula ya ce, kaso saba’in da biyar cikin dari na wadanda suka yi zabe mata ne da matasa, sai dai yawancin lokuta ba a tafiya da su a cikin sha’anin gudanar da mulki, duk da cewa akwai mata da matasa da dama a cikin al’umma wadanda suka cancanci a tafiyar da mulki tare da su.

Ya kara da cewa kan hakan ne kungiyar ta shirya taron matasan jihar Kano, wanda kungiyoyin matasa sama da guda dari zasu halarta don tattauna matsalolin matasa tare da lalubo hanyoyin magance su.

A cewar Mukhtar Dauda Raula Kano Youths Political Forum kungiya ce da ‘ya’yan manyan ‘yan siyasar jihar Kano dake jam’iyyu daban daban suka kafa da nufin kawar da siyasar daba, zagi da cin mutunci, a don haka taron zai maida hankali ne wajen wayar da kan matasa yadda zasu shiga a dama da su a harkokin siyasa tare da fadakar da su illar shaye-shaye da siyasar daba.

A nasa bangaren Shugaban tashar Freedom Radio dake kano, Alhaji Ado Saidu Warawa ya shawarci kungiyar da su rinka daukar matsalolin matasa daya bayan daya don lalubo hanyoyin magance su, inda ya bayyana cewa Freedom zata baiwa kungiyar duk gudunmawar da ta dace wajen ganin ta samu nasarar cinma burinta.

Taron dai zai gudana ne a ranar 26 ga watan Disamba da muke ciki a dakin taron na gidan marigayi Malam Aminu Kano wato Mumbayya House.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!