Labarai
Majalisa ta aikewa hukumar tattara haraji ta FIRS takardar tuhuma
Majalisar dattijai ta aika da takardar tuhuma ga hukumar tattara haraji ta kasa FIRS, sakamakon zargin hukumar da kin sanya wasu kudade da ta karbo daga ma’aikatu da hukumomi da kuma sassan gwamnati a cikin asusun tarayya.
A cewar Majalisar kudaden dai sun kai naira tiriliyan daya da biliyan dari hudu.
Takardar tuhumar ta biyo bayan rahoton babban mai binciken kudi na tarayya na shekarar dubu biyu da goma sha biyar, wanda aka mika shi ga shugaban kwamitin sanata Mathew Urhoghide.
Kwamitin dai yana gudanar da bincike ne kan kudaden da hukumomin gwamnati suka kashe cikin shekaru biyar da suka gabata.
You must be logged in to post a comment Login