Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An ceto mutane da aka sace a tsakanin Kaduna zuwa Abuja – El- Rufa’I

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojoji sun samu nasaran ceto mutane tara daga cikin wadanda aka sace a jiya lahadi akan titin Kaduna zuwa Abuja.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan harkokin tsaron cikin gida Samuel Aruwan ya fitar jiya a Kaduna.

Sanarwar ta ce sojojin yayin wani rangadi a yankin Akilubu-Gidan Busa ne suka samu nasaran ceto mutanen.

A jiya lahadi ne dai ake zargin ‘yan bindinga suka sace mutanen bayan da suka tare wata motar safa mai daukar mutane goma sha takwas akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!