Labarai
Majalisa ta aikewa ministan kudin Najeriya takardar gayyata
Kwamitin kula da harkokin kudi na majalisar dattijai ya gayyaci ministan kudi Hajiya Zainab Ahmed domin tayi bayani kan yadda gwamnatin tarayya take kashe kudadan kwangilar ayyukan tituna da yakai kimanin tiriliyon 2.7.
Daga cikin wadanda za su bayyana a gaban kwamitin sun hada da ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola da babban akanta na kasa Ahmed Idris tare da Managing Darakta na hukumar kula da kadarorin gwamnati Uche Orji.
Shugaban kwamitin ya bayyana gayyatar yayin da yake ganawa da manema a birnin tarayya Abuja.
Ayyukan titin sun hada da Kano zuwa Abuja da kuma titin Lagos Ibadan da kuma titin second Niger Bridge wanda maaikatun ayyuka da na kudi da hukumar kula da jarin kasar nan ke kula da aikin kula da titinan a kasar nan.
Da yake wa kwamitin jawabi shugaban hukumar kula da jarin kasar nan Uche Orji yace gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin shugaban kasa da zai kula da manyan ayyuka tare da ganin yadda ake basu kudade tun a watan Fabrairu shekara ta dubu biyu da sha takwas.
Mr Orji ya kara da cewa izuwa yanzu ayyukan titinan uku sun lankwame kudi kimanin naira biliyan dari biyu da talatin da daya.
You must be logged in to post a comment Login