Connect with us

Labarai

An sanya ranar rubutu jarrabawar Common Entrance

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce a ta sanya ranar 17 ga watan Okotoba a matsayin ranar da ‘yan aji shida na firamare za su rubutu jarrabawar Common Entrance a sassan kasar nan.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi ta kasa Ben Goong ya fitar a jiya Laraba.

Ta cikin sanarwar karamin ministan ilimi Emeka Nwajiuba ya ce jarrabawar wacce ake yin ta a rana guda zai baiwa dalibai damar shiga makarantun hadaka takasa da sauran makarantu na gwamnati da masu zaman kan su a bana.

Akan haka ne ministan ya umarci dukkanin hukumomin shirya jarrabawa da su tsara jadawalin su nan da kwanaki 7 kafin fara jarrabawar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 330,179 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!