Connect with us

Labarai

Sallah : Yadda matan Kano suka cika gidajen yin kunshi da kitso

Published

on

A ya yin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar bukukuwan babbar sallah suma mata ba’a barsu a baya ba, domin ana su bangaren suna ci gaba da shirye shiryensu musamman wajen yin kunshi da shirin yadda za suyi suyar nama.

Duk da kasancewar hukumomi nata kiraye-kiraye kan cewa jama’a su zauna  a gidajensu, yayin bukukuwan sallah domin dakile cutar Corona a nasu bangaren mata iyaye na gida na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar bikin na sallah.

Yayin da wasu ke zuwa gidan kunshi da kitso wasu kam siyan kayyakin kamshi da zasu gudanar da suyar nama suke.

Freedom rediyo ta tattauna da wasu mata kan yadda suke gudanar da shirye-shiryensu na sallah.

Haka zalika wasu mata da Freedom Radiyo ta iskesu a gidan kunshi sun bayyana cewa akwai cunkoso a mafi yawa na gidajen kitso da suka ziyarta.

Hajara Ya’u Haruna wata macece da ta ke sana’ar kunshi ta bayyana cewar cuta Corona ta yi mata illa sakamakon cewa ba ta samun abokan hulda kamar yadda ta ke samu a shekarun baya.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta rawaito cewa, Malama Hajara Ya’u ta kuma ce tun kimanin sallah saura sati daya ta ke gudanar da sana’ar ta kunshin

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,753 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!