Connect with us

Labarai

Majalisa ta nemi Buhari ya mayar da Nasir Argungu kan mukamin sa

Published

on

Majalisar wakilai ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta mayar da Nasir Argungu akan mukaminsa na shugabancin hukumar samar da aikin yi ta kasa NDE.

‘Yan majalisar sun yi wannan kiran ne a yau talata, bayan da dan majalisa Olajide Olatunbosun mai wakiltar mazabar Atisbo/Saki East/Saki a jihar Oyo ya gabatar da bukatar hakan.

Tun farko dai mamban ya gabatar da kudirin ne game da guraben aiki na wucin gadi na gwamnatin tarayya guda dari bakwai da saba’in da hudu, wanda majalisar ta samu sabani da karamin ministan kwadago da samar da aikin yi, Festus Keyamo.

‘Yan majalisar dai sun soki matakin da shugaban kasa ya dauka na korar shugaban hukumar ta NDE daga mukaminsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!