Ƙetare
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana alhini kan rikice-rikicen Sudan da yankin Sahel

Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ta bayyana alhini kan yadda rikice-rikicen da ke faruwa a kasar Sudan da ma yankin Sahel Baki daya.
tana tana Mai bayyana Hakan a Matsayin gazawar duniya wajen ɗaukar mataki da ya dace Domin dakatar da zubda jinin Wadanda ba suji ba basu gani ba.
Ta ce, irin wannan gazawa na ci gaba da addabar al’ummar duniya inda har ta kai ga cewa ba ta iya samun barci da daddare, sakamakon yadda ake barin mutane cikin mawucin hali sakamakon rashin tsaro.
Sannan ta jaddada cewa wajibi ne kasashen duniya da su ɗauki matakai na gaggawa domin kare fararen hula.
You must be logged in to post a comment Login