Ƙetare
Majalisar ɗinkin duniya ta buƙaci a gaggauta tsagaita wuta a Gaza

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya bukaci da a gaggauta tsagaita wuta a Gaza, bayan da Isra’aila ta ce ta fara kai farmaki domin ƙwace birnin Gaza.
Guterres, ya ce, ya na da matuƙar muhimmanci a kiyaye da kashe-kashe da kuma lalata duƙiyar da wannan farmaki zai haddasa.
Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da fara kai matakin farko na farmakin a Gaza, inda firaiministan ƙasar Benjamin Netanyahu ya ce yunkuri ne na ganin ya ƙwace abin da ya kira waje na karshe a Gaza.
Jami’ai a Gaza sun ce dubban Falasɗinawa na tserewa birnin wanda Mutane fiye da miliyan guda ke rayuwa a cikinsa.
You must be logged in to post a comment Login